Min menu

Pages

News Sports

Muhimman Abubuwan Da Suka Faru A Duniyar Nishadi Ta Najeriya A 2022

A makon nan ne muke bankwana da shekarar 2022, kuma kamar sauran shekarun da suka gabata, abubuwa da dama sun wakana a Najeriya, ciki har…


A makon nan ne muke bankwana da shekarar 2022, kuma kamar sauran shekarun da suka gabata, abubuwa da dama sun wakana a Najeriya, ciki har da masana’antun fina-finai na na Kannywood da Nollywood.

Aminiya ta yi waiwaye domin zakulo wasu muhimman abubuwan da suka faru a masana’antun da suka fi daukar hankalin mutane a wannan shekarar da take nade tabarma.

Dambarawar Nafisa da Sarkin Waka

A watan Janairun 2022 ne aka wayi gari fitacciyar jarumar fina-finan Hausar nan, kuma daya daga cikin manyan jarumar fim din nan mai dogon zango na Labarina, Nafisa Abdullahi ta ce za ta daina fitowa a cikin shirin.

Jarumar ta ce ta yanke shawarar daukar matakin ne saboda ta samu isasshen lokacin gudanar da harkokin kasuwancinta da kuma na karatu.

Nafisa ta tabbatar da hakan ne a cikin wani sako da ta wallafa a shafinta na Instagram, inda ta ce tana mai matukar takaicin yin hakan.

Yayin da ake ci gaba da ce-ce-ku-ce kan wannan batun kuma, sai wata muhawarar ta sake barkewa tsakaninsu kan batun tarbiyya, duk da Nazirun ya ce sam ba da jarumar yake ba.
You may also like


Mutane da dama sun yi ta fashin bakin cewa kalaman Nazirun, wanda ake yi wa lakabi da Sarkin Waka gugar zana ne ga Nafisan.

Sai dai bayan lamarin ya dauki zafi, Naziru ya ce shi ba da Nafisat yake yi a wani sakon murya da ya aika da Aminiya ta samu.

Kalaman da fitaccen mawakin yayi na cewa idan ana neman ’ya’yan da iyayensu suka kasa kula da su a zo masana’antar ta fim ne dai abin da ya kara rura wutar rikici a tsakaninsu.

Sarkin Waka ya wallafa hakan ne a shafinsa ma Instagram da Facebook a wancan lokacin .

Ganduje ya nada Naburaska mai ba shi shawara a bangaren ‘Farfaganda’

A watan Janairun ne dai Gwamnan Jihar Kano, Abdullahi Umar Ganduje, ya nada fitaccen jarumin nan na masana’antar Kannywood, Mustapha Naburaska a matsayin mai ba shi shawara kan ‘Farfaganda’.

Jarumin, kuma mai shirya fina-finai a masana’antar, Falalu A. Dorayi ne ya sanar da nadin a shafinsa na Instagram, inda ya taya shi murnar samun matsayin.
You are now in the last article

Comments

    "+html+"
"; document.querySelector("#tocDiv").innerHTML = Xhtml; document.querySelectorAll(".ScrolingToTarget").forEach(function(asd){ asd.addEventListener("click", function(e){ e.preventDefault(); document.querySelector(asd.getAttribute('href')).scrollIntoView({ behavior: 'smooth' }); });}) if (document.querySelectorAll('.amp-contnt h1,.amp-contnt h2, .amp-contnt h3, .amp-contnt h4').length == 0){ document.querySelector('ul#tocList').innerHTML = "
No titles
"; } document.querySelector('.closetoc').addEventListener('click', function(x){ document.querySelector('.topcs7v').classList.toggle('closed') }); }